in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta sa kaimi ga kyautata muhalli, in ji firaminista Li Keqiang
2014-04-21 11:02:01 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jagoranci taro karo na farko na sabon kwamitin kula da harkokin makamashi, inda aka tattauna kan manyan tsare-tsare, da manyan ayyukan da suka shafi raya makamashi.

Yayin taron na ranar 18 ga watan nan, Mr. Li ya ce batun samar da isasshen makamashi yadda ya kamata, da kuma tabbatar da tsaron sa, yana da nasaba da yunkurin zamanantar da kasar Sin. Kuma kamata ya yi a mai da raya kasa bisa kimiyya wani babban ginshiki.

Har ila yau Mr. Li, ya ce bisa la'akari da halin da ake ciki a yanzu, ya dace a dauki matakan da suka dace, da sa kaimi ga yin gyare-gyare a fannin samar da makamashi da amfani da shi.

Sauran matakan da firaministan ya zayyana sun hada da karfafa kwarewar kasar Sin wajen raya tsimin makamashi, da daukar matakai na yaki da gurbata muhalli, ciki hadda magance yawaitar gurbatacciyar iska, tare da rage yawan gurbatacciyar iska da tsimin makamashi, da sa kaimi ga inganta muhalli mai tsabta, da bin hanyoyin raya makamashi cikin dogon lokaci, ta yadda za a iya bayar da taimako ga bunkasuwar tattalin arziki.

Li ya kara da cewa, a matsayin ta na babbar kasa mai tasowa, yawan makamashin da Sin ke bukata zai karu. Sakamakon haka ya kamata a mai da hankali ga dogaro da karfin kasar a gida, don inganta kwarewar samar da makamashi. A sa'i daya kuma kamata ya yi a kara hada kai da kasashen duniya, da daga matsayin kasar a fannin samar da ingantaccen makamashi, da kiyaye tsaron sa. Bugu da kari akwai bukatar ba da fiffiko ga manyan tsare-tsare na tsimin makamashi, don rage yawan makashi da kasar ke amfani da shi, matakin da zai taimaka wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China