Mahukuntan jihar dai sun dauki wannan mataki ne, da nufin kyautata muhalli, da bunkasa biranen jihar da kuma sassauta matsalar karancin makamashi.
Olusosun, cibiyar shara ce mafi girma a Legas, wadda ke fitar da sinadarai masu yawa da ake sarrafawa, tare kuma da canza su zuwa iskar gas ta methane.
Da fari a kan tattara bolar ne a kai ta wurin sarrafawa, daga nan kuma a samar da wutar lantarki ta amfani da isakar ta methane ga mazauna wurin. An ce dagwalon da ake fitarwa ma wajen tashe bolar ana amfani da shi ga shuke-shuke.
Bayan samun nasarar wannan shiri a matakin gwaji, yanzu haka ana fadada shi a sassan jihar ta Legas daban daban. (Bilkisu)