in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya yi kiran da dana tarkon yaki da ayyukan ta'addanci a Xinjiang
2014-05-29 20:28:12 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kiran da a baza tarkon da zai kai ga dakile ayyukan ta'addanci a yankin Xinjiang.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, manufar daukar wannan matakin, ita ce samar da zaman lafiya cikin dogon lafiya a yankin.

Xi ya bayyana hakan ne yayin taron yini biyu kan nazarin wasu ayyuka masu muhimmanci game da jihar na Xinjiang da ke arewa maso yammacin Sin wanda aka kammala a yau.

An gudanar da taron ne,yayin da jihar ta fuskanci wasu jerin munanan hare-haren ta'addanci,ciki har da wanda aka kai a wata kasuwa ranar 20 ga watan Mayu a garin Urumqi,babban birnin jihar, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 39,kana wasu 94 suka jikkata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China