in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da aikin yaki da ta'addanci musamman na tsawon shekara daya a jihar Xinjiang
2014-05-24 16:28:59 cri
A Jumma'a 23 ga watan da muke ciki, gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashinta ta kasar Sin ta kira taro ta kafofin sadarwa da talibijin, inda ta sanar da cewa, bisa izinin da ta samu daga gwamnatin tsakiya ta kasar, da kudurin da rukunin ba da jagoranci kan aikin yaki da ta'addanci ta kasar ya yi da kuma hali mai tsanani da ake ciki a jihar, gwamnatin jihar ta kudurta cewa, tun daga ran 23 ga watan nan zuwa watan Yunin shekarar ta 2015, za a gudanar da aikin yaki da ta'addanci musamman a jihar Xinjiang, domin kokarin shawo kan 'yan ta'adda baki daya a jihar, ta yadda za a iya kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar da odar zaman al'ummar jihar kamar yadda ake fata.

Bayan harin ta'addanci da ya haddasa mutuwar mutane 39 da raunana wasu da dama a wata kasuwar birnin Urumqi na jihar Xinjiang ta kasar Sin a ran 22 ga wata, wasu kafofin yada labaru na kasashen duniya sun mai da hankali sosai kan lamarin. Gidan talibijin na Denver na kasar Amurka da mujalla "The Diplomat" ta Japan da tarayyar kamfanin dillancin labaru na Pakistan sun ce, yin yaki da ta'addanci ya zama wani batun da dukkan al'ummomin duniya suke fuskanta tare saboda yanzu fararen hula sun zama burin da 'yan ta'adda suke kai farmaki. Matsalar ta'addanci a kasar Sin ba wata matsalar cikin gida ta kasar Sin kadai ba ce, matsala ce ta duniya baki daya. Ya kamata al'ummomin duniya su yi kokarin tare wajen kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China