in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aziz ya yi tazarce a matsayin shugaban kasar Mauritania
2014-06-23 11:03:07 cri
Sakamakon zaben shugaban kasar Mauritania da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta fitar a ranar 22 ga wata, ya nuna cewa, shugaban kasar na yanzu Mohamed Ould Abdel Aziz ya cimma nasarar samun zarcewa a karo na biyu.

Bisa sakamakon da aka bayar, an ce, Aziz ya samu kuri'u dubu 578 a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 21 ga wata, kuri'un da suka kai kashi 81.89 cikin dari. Yayin da kuma Mr Abed wanda ke biye masa a matsayi na biyu a zaben, ya samu kuri'u dubu 60 da yan kai, adadin da bai wuce kashi 8.67 cikin dari kacal ba.

Bisa kididdigar da hukumar zaben kasar ta yi, an ce, yawan kuri'un da aka jefa a zaben na wannan karo a tsakanin jama'ar kasar ya kai kashi 56.46 cikin dari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China