Wadannan kudade za su taimakawa wajen cigaban wannan tsari da aka jima ana aiwatarwa a kasar Mauritaniya dake taimakawa, a kan kudin Ouguiyas 5000 kwatankwacin dalar Amurka 20 za a iya daukar nauyin gudanar da wasu bincike da bada kulawa ga mata masu juna biyu.
A cewar ministan kiwon lafiya na kasar, dokta Ba Housseinou Hamamdy, wannan taimakon kudi na AFD zai tallafa ga bunkasa da kuma karfafa manufar kasa ta bada rangwame ga mata, da kuma cika gibin taimakon da ya wuce kan tsarin kasa na lafiyar uwa da dan ta, wanda ya taimaka ga tafiyar da aikin a cikin yankuna 6 na cikin kasar.
Tare da samun mutuwar mata 686 wajen haihuwa a cikin haihuwa 100,000 da kuma mutuwar yara 122 a cikin haihuwa 1000, mutuwar uwa da dan ta ta kasance babbar matsala da gwamnatin kasar Mauritaniya ke maida hankali sosai kanta in ji minista Hamamdy. (Maman Ada)