Wadannan manyan ayyuka sun shafi ' samar da makamashi da kuma daidaita tsarin samar da wutar lantarki a wasu yankuna 20 na kasar' ta yadda mutane 200,000 zasu amfana a cewar wasu takardu. Bikin sanya hannu kan wadannan takardu da suka shafi wannan yarjejeniya an yi shi ne a ranar Litinin a birnin Nouakchott tsakanin Taleb Ould Abdival ministan fetur da makamashi na Mauritaniya da Hans-Georg Gerstenlauer wakilin EU a Nouakchott. (Maman Ada)