A yayin taron, Mr. Li Keqiang ya nuna cewa, kasar Sin kasa ce dake kokarin tsare tsarin tattalin arziki da na kudi da yake kasancewa a duniya yanzu, kuma za ta ci gaba da taka rawar da ta dace kamar yadda ta saba yi, har ma tana son hada kan bangarori daban daban domin ba da gudummawarta wajen kara kyautata tsarin tattalin arziki da na kudi na kasa da kasa.
A nasa bangaren, Mr. Cameron ya ce, ya kamata kasashen duniya su kara yin hadin gwiwa kan yadda za a hanzarta kyautata tsarin tattalin arziki, yin cinikayya cikin 'yanci, da kokarin hana bullowar hanyoyin ba da kariya iri iri domin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba.
Sannan madam Christine Lagarde da sauran shugabannin kungiyoyin kudi na kasa da kasa sun yaba da muhimmiyar gudummawa da kasar Sin ta bayar wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa, da kyautata tsarin tattalin arzikin kasa da kasa da kuma mayar da kudin Renminbi da ya zama kudin kasa da kasa. Dukkansu sun bayyana cewa, kungiyoyinsu za su kara nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa da su kara yin hadin gwiwa tsakaninsu. (Sanusi Chen)