in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wajibi ne Afirka ta samu kujerar din din din a majalisar dinkin duniya, in ji shugaban kasar Zambia
2012-09-26 11:09:12 cri

Shugaban kasar Zambia Michael Sata, ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka, da su tashi tsaye wajen fafitikar samar wa nahiyar kujerar din din din a hukumar tsaro ta majalisar dinkin duniya.

Wata kafar yada labarai ta kasar Zambia mai suna ZANIS, ta rawaito shugaban kasar na wannan kira, yayin da yake tsokaci gaban mahalarta taron majalisar ta tsaron da aka shirya domin tattauna batutuwa masu alaka da kare doka da oda.

Sata ya kara da cewa, wannan bukata ta yi daidai da kudurin kwamitin da kungiyar tarayyar Afirka AU ta kafa, dake bukatar samarwa nahiyar kujerun din din din guda 2 a majalisar ta tsaro, baya ga wasu karin kujerun 2 domin baiwa nahiyar cikakkiyar damar shiga a dama da ita, a fagen shawarwarin da suka shafi harkokin kasa da kasa.

"Tun kafuwar wannan majalisa kawo yau, nahiyar Afirka na cigaba da zamowa 'yar kallo, maimakon abokiyar shawara, kawo yanzu ba mu da wata kujera ta din din din, duk kuwa da wakilcin kasashe 54 da muke da shi, don haka ba zai yiwu a yi batun kare doka da oda ba, muddin dai babu mutunta kimar juna, lokaci ya yi da dukkanin kasashen Afirka za su mike tsaye, domin tabbatar da nasarar samun wannan kujera ta din din din". A ma'anar kalaman shugaban kasar Zambia Michael Sata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China