in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambia ya bukaci sashen lantarkin kasarsa da ya yi hadin gwiwa da Sin
2013-12-05 11:06:31 cri

Shugaba Michael Sata na Zambia ya yi kira ga sashen samar da lantarki na kasarsa, da ya yi cikakken amfani da damar hadin gwiwa da kasar Sin, wajen samar da isasshen lantarki da zai ishi al'ummar kasar baki daya.

Shugaba Sata, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, a jawabinsa na bikin bude sabon sashen tashar samar da lantarki ta arewacin Kariba, wadda wani kamfanin kasar Sin ya aiwatar, ya kara da cewa, wajibi ne kamfanin lantarki na Zesco mallakar kasar, ya tabbatar da al'ummar kasar sun samu isasshen lantarki.

Ya ce, gwamnatinsa na iyakacin kokarin samar da lantarki ga kowa da kowa, wanda hakan ne ma ya sanya ta gudanar da sabbin ayyuka da suka shafi wannan fanni.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, kamfanin kasar ta Sin wanda ya kammala zangon farko na wannan aiki, da zai samar da lantarki megawatts 180, tuni ya shiga aikin sashe na biyu, wanda ake sa ran kammala shi nan da watan Maris na shekara mai zuwa.

An ce, bankin bunkasa ayyukan shige da fice na kasar Sin ne ya samar da kudi kimanin dalar Amurka miliyan 315, yayin da bankin bunkasa ci gaba na Afirka ta Kudu ya samar da dala miliyan 105 domin wannan aiki da aka fara shi tun cikin shekarar 2008. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China