140613-firaministan-sin-zai-kai-ziyara-nahiyar-turai-zainab.m4a
|
A jiya Alhamis ne dai mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Chao, ya bayyanawa taron manema labaru cewa, ziyarar da Li Keqiang zai gudanar a wannan karo za ta bada damar cimma nasarori masu yawa, tare da sakamako mai kyau.
Game da batun maida birnin Landan matsayin cibiyar cinikayyar kudin Sin, da kuma bunkasuwar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Ingila a fannin hada-hadar kudi kuwa, wata jami'ar ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta yi imanin cewa, ziyarar ta wannan karo za ta haifar da ci gaba kan batun.
Wannan dai ziyarar da firaminista Li Keqiang zai kai kasar Birtaniya ta zo gabar da ake cika shekaru 10, da kafuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da kasar Birtaniya bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. Kuma wannan ne karo na farko da sabon firaministan kasar Sin zai kai ziyara a Ingila, kana karo na farko da firaministan na Sin zai ziyarci kasar a cikin shekaru 3 na baya bayan nan. Hakan ne kuma ya sanya ziyarar matukar janyo hankalin kasa da kasa.
A cewar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Chao, wannan ziyara za ta bada damar bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da shigar da sabbin batutuwa yayin da ake raya dangantakar su.
Wang Chao ya ce, "A yayin ziyarar firaminista Li Keqiang a kasar Ingila, ana fatan kara inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, musamman a fannonin gina ababen more rayuwa, da samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya, da harhar sufurin jiragen kasa masu sauri, da hada-hadar kudi, da fasahohin zamani da dai sauransu. Kana za a nemi sabuwar hanyar inganta hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.
Haka zalika za a kara hadin gwiwa a fannin al'adu, don tabbatar da tushen al'umma dake inganta dangantaka."
Har wa yau yayin ziyarar, Li Keqiang zai gana da sarauniyar kasar Ingila Elizabeth II, zai kuma yi shawarwari tare da firaministan kasar David Cameron, inda daga bisani za su gudanar da taron manema labaru, don fayyace hanyar da za a bi wajen zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen su, da kuma kara hadin gwiwarsu.
Ban da wannan kuma, Li Keqiang zai yi jawabi ga kungiyar masana mafi tasiri ta kasar Ingila, inda zai yi bayani game da halin bunkasuwar tattalin arzikin Sin, da ra'ayin Sin kan halin da ke ciki a duniya, da kuma bada shawara kan yadda za a inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Ingila.
A hannu guda kuma birnin Landan na kasar Birtaniya, wanda kuma ke matsayin daya daga manyan cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya, a wadannan shekaru Sin na kokarin sa kaimi ga manufar amfani da kudin Sin tsakanin kasashen duniya. Don haka, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Ingila a wannan fanni, ya janyo hankalin kasa da kasa.
Game da hakan mataimakiyar ministan ciniki na Sin Gao Yan ta bayyana cewa, "Birnin London yana kokarin kasancewa cibiyar musayar kudin Sin, kana Sin tana tattaunawa tare da Birtaniya a wannan fanni. An kuma yi imani da cewa, za a samu babban ci gaba a wannan fanni, karkashin ziyarar da Mr. Li Keqiang zai gudanar a wannan karo."
Ita ma kasar Girka muhimmiyar kasa ce dake hadin gwiwa da Sin a cikin jerin kasashe mambobin kungiyar EU. A fakon rabin shekarar bana, kasar ta Girka ta fara jagorantar kungiyar EU bisa tsarin karba karba, inda ta bayyana cewa, tana fatan taka muhimmiyar rawa wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen Turai da kasar Sin. Wang Chao ya bayyana cewa, ta hanyar ziyarar da Li Keqiang zai yi a kasar Girka, za a kara sada zuminci, da fahimtar juna a fannin siyasa, da kuma fadada hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. Wang Chao ya ce, "Kasashen biyu za su bayar da hadaddiyar sanarwa, za kuma su daddale yarjejeniyoyi da dama a tsakanin gwamnatocin sassan biyu, da fannoninsu masu alaka da samar da ababen more rayuwa, da sashen al'adu, da harkokin sufurin teku, tare da ingancin sarrafa kaya da dai sauransu." (Zainab)