Babban sakataren MDD ya taya wa Iraki murnar kammala zaben 'yan majalisar dokokin kasar
Jiya Alhamis daya ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ba da sanarwar taya murna ga jama'a da gwamnatin Iraki da su gudanar da zaben majalisar dokokin kasar da zaben majalisar dokokin yankin Kurdawa mai cin gashin kansa, tare da nuna yabo kan kokarinsu na kara farfado da tsarin demokuradiya a cikin kasar.
A ranar 30 ga watan Afrilun da ya gabata ne, kasar Iraki ta gudanar da zaben sabuwar majalisar dokokin kasar wanda ya zama karo na uku da aka gudanar da irinsa tun bayan yakin Iraki a shekarar 2003, kuma karo na farko da aka yi tun bayan janyewar sojojin Amurka daga Iraki a karshen shekarar 2011. 'Yan takara sama da 9000 sun yi takarar kujeru 328 na sabuwar majalisar dokokin kasar.(Fatima)