"yau hukumar FAO ta yi wannan kira, duk da cewa, ana samun daidaito kan yadda za a samar da abinci mai inganci da kuma hanyoyin ci gaba, amma samar da kudi ya kasance wata babbar matsala", cewar Nesirky a gaban manema labarai. Ya kara da cewa, misali mai bada tsoro shi ne FAO ta rasa samun kudi wajen gudanr da ayyukanta a yankin Sahel da yankin Kuryar Afrika.
Kamar yadda Nesirky ya ce, babban jami'in hukumar FAO ya damu matuka game da rashin damar taimakawa mutanen da ke cikin bukata a yankin Kuryar Afrika.
Nesirky ya kuma nuna cewa, a lokacin da yake jawabi a yayin taron tattalin arziki na kasa da kasa a birnin Madrid na kasar Spain, Jose Graziano da Silva, babban direktan hukumar FAO ya furta cewa, a yankin Kuryar Afrika, hukumar tana rashin damar kara samun nasarorin da za su taimaka wajen kawar da bala'in karancin abinci da ya faru a shekarar bara a kasar Somalia, lamarin ya kara karya kwarin gwiwar iyalai da dama da ke fuskantar bala'in fari. (Abdou Halilou)