Gidauniyar za ta rika samun kudaden da za ta gudanar da aikinta daga kasashen dake fitar da man fetur.
"Mun sanya kira domin ganin an tabbatar da kafa wannan asusun da zai samu kudi daga kasashen dake fitar da man fetur da ma'adinai, ta yadda za mu samu damar tinkarar matsalar karancin abinci a yankin Sahel da kuma cikin kusurwar Afrika." in ji mista Jose Graziano Da Silva a yayin wani zaman taron shiyya na hukumar FAO kan nahiyar Afrika karo na 27 da aka gudanar a birnin Brazaville. (Maman Ada)