An shirya taron yaki da ta'addanci na duniya karo na farko a ran 12 ga watan nan, a fadar 'Palace of the Republic' da ke a birnin Bagadaza, inda aka taunawa halin da ake ciki a fagen yaki da ta'addanci a Iraki, da hadin kan kasar, da sauran kasashe wajen yaki da ta'addanci.
Firaministan kasar Iraki Nuri Kamal al-Maliki ya bayyana a gun bude taron cewa, hare-haren ta'addanci da ke aukuwa a Iraqi a halin yanzu, ba su da alaka da bambancin kabilu da addinai, don haka ya kamata bangarori daban daban, su hada kansu domin yaki da ta'addanci. Har ila yau Al-Maliki ya yi kira ga kasashen duniya, da su inganta hadin kai a fannonin tsaro da musayar bayanai, domin yaki da ta'addanci tare.
Maliki ya kara da cewa, tashe-tashen hankulan da suke ci gaba a kasar Sham, sun kawo babbar illa ga zaman lafiyar shiyyar da take ciki, muddin kuma ba a kawo karshensu cikin sauri ba, ayyukan ta'addanci na iya bazuwa.
Wakilan da suka samu damar halartar taron na yini Biyu sun hada da na kasashe da yankuna 25, da MDD, da kungiyar tarayyar Turai EU, da kawancen kasashen Larabawa wato LA. Sauran wakilan sun hada da na kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU, da hukumar 'yan sanda ta duniya da dai sauransu.
Ana dai sa ran tattauna batutuwan da suka shafi hanyoyin da kungiyoyin 'yan ta'adda ke bi wajen samun makamai da kudade, da kuma halin da ake ciki a fagen yaki da ta'addanci a Iraki, da ma hadin kan kasar, da kuma sauran kasashe wajen yaki da ta'addanci. (Danladi)