Majalisar dokokin kasar Afrika ta Kudu ta sanar a kwanan nan cewa tana shirin kafa wani kwamitin hadin gwiwa da za'a aza ma nauyin gudanar da bincike kan zaton sama da fadi da kudin kasa domin gudanar da ayyukan zamanintar da wani gidan shugaba Jacob Zuma. Shugaban majalisar dokoki Max Sisulu ya jaddada cewa wannan kwamiti zai kunshi mambobi goma sha biyu da suka hada da mambobi bakwai na jam'iyyar ANC dake mulkin kasa, mambobi biyu na jam'iyyar adawa ta DA, mamba guda na jam'iyyar IFP, mamba guda daga jam'iyyar CODE da kuma a karshe mamba guda da zai wakilci kananan jam'iyyun siyasa takwas.
Kwamitin zai gabatar da sakamakonsa a kalla nan da ranar 30 ga watan Afrilu. (Maman Ada)