A wannan rana, yayin da Sassou ke halartar bikin cika shekaru 25 da amfani da yarjejeniyar Brazaville a hedkwatar kasar, ya bayyana cewa, yanzu, jama'ar kasar Afrika ta Tsakiya na shan wahala, kasashen duniya na da hakkin ci gaba da daukar matakai, don kawo karshen rikici a cikin wannan kasa. Ya sanar da cewa, za a kafa wani asusun zaman lafiya, don nuna goyon baya game da aikin sake gina yankunan kasashen Afrika da ke fama da yake-yake.
A ranar 13 ga watan Disamba na shekarar 1988, kasashen Angola, Cuba, da Afrika ta kudu sun daddale wata yarjejeniya a birnin Brazaville, inda suka amince da bin ka'idar warware rikici a yankunan yammaci da kudancin Afrika cikin lumana, don kawo karshen rikice rikicen soja da ake fama a shiyyar.(Bako)