An bude taron koli na kungiyar kasuwannin bai daya ta gabashi da kuma kudancin Afirka karo na 17, a birnin Kinshasa, babban birnin kasar Kongo(Kinshasa). Taron wanda zai gudana daga ranar 26 zuwa 27 ga watan nan, ya samu halartar shugabanni da wakilai na kasashen mambobin kungiyar 19.
Abubuwan da aka sanya gaba yayin wannan taron koli, sun hada da kaddamar da yankin cinikayya cikin 'yanci na kungiyar, da sa kaimi ga bunkasuwar kawancen kula da harkokin harajin hukumomin kwastan.
Haka zalika za a gudanar da shawarwari tsakanin bangarori uku na kungiyar, da kungiyar gamayyar gabashin Afirka, da kungiyar gamayyar raya kudancin Afirka. Sai kuma batun kyautata tsaro da zaman lafiya, da bunkasa samar da ababen more rayuwar al'umma, da aikin gona, da muhalli da dai sauran muhimman batutuwa.
A wannan karo shugaban kasar Kongo(Kinshasa) Joseph Kabila, ya maye gurbin takwaransa na kasar Uganda Yoweri Museveni, wanda a baya, shi ne ke jagorantar kungiyar kasuwar bai daya ta gabashi da kuma kudancin nahiyar ta Afirka.(Danladi)