Mr. Blatter wanda ya gabatar da sakon taya murnar ta sa, ta hannun shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Uganda Moses Magogo a ranar juma'ar da ta gabata, ya ce lashe wannan gasa da KCCA ya yi a karo na 10 abun a yaba ne. Ya kuma jinjinawa kulaf din bisa yadda ya nishadantar da masoya wasan kwallon kafa dake kasar.
Game da hakan dai kocin KCCA George Nsimbe ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yayi farin ciki da samun sakon Mr. Blatter, wanda saboda yawan ayyukan da ke gaban sa, ba kasafai yake iya samun damar taya kulaflikan nahiyoyi, murnar nasarorin da suke samu ba.
Koda yake dai kulaf din na KCCA bai taka wata rawar a zo a gani ba a yayin gasar cin kofin zakarun nahiyar a bana, ana sa ran ganin ya yi wani hobbasa a gasar ta badi.
Yayin gasar zakarun nahiyar Afirka dai na bana, KCCA ta lashe kulaf din El-Merreikh na kasar Sudan, kafin kuma Nkana FC na Zambia ya fidda ita a zagayen farko na gasar. (Saminu Alhassan)