in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayern Munich ta dau kofin Jamus bayan lashe Dotmund da ci 2 da nema
2014-05-20 14:59:20 cri
Bayern Munich ta lashe Dortmund da ci 2 da nema a wasan da kuloflikan 2 suka yi ranar Asabar 17 ga wata, matakin da ya bata damar daukar kofin kasar Jamus, wanda ya zama kambi na 2 da kungiyar ta samu a kakar wasanni ta 2013/2014, bayan da ta zama zakaran gasar Bundesliga.

Har ila yau dai wannan nasarar ta sanya Bayern din kaiwa ga samun wannan nasara a karo na 17, kuma karo na 10 da ta samu kambi 2 na gasannin kwallon kafan kasar Jamus a kakar wasa guda.

Yayin wasan da aka buga a filin wasan Olympia dake birnin Berlin, kulob din na Bayern Munich ya fi kai yawan hare-hare gidan kungiyar Dortmund, sai dai bayan dawowa hutun rabin lokaci Dortmund ta kara kwazo, a kokarin ta na kutsa kai harabar gidan Bayern. Sai dai duk da hakan kungiyoyin 2 ba su samu zarafin sanya kwallo a raga ba, haka kuma aka tashi canjaras kowa na nema.

Bayan an dawo zangon farko na karin lokaci ne wasan ya sauya, inda dan wasan Bayern Arjen Robben ya samu jefa kwallo a ragar Dortmund, cikin minti na 107, kafin Thomas Mueller ya kara kwallo ta biyu bayan 'yan mituna kadan, aka kuma tashi Bayern Munich na da kwallo biyu Dortmund kuma na nema.

Kocin kungiyar Bayern Munich Pep Guardiola ya nuna farin cikinsa ga yadda 'yan wasansa suka samu damar lashe wasan, ganin yadda hakan ya zama karo na biyu, da kungiyar ta lashe babbar gasar kasar, a kuma cikin shekara daya da Guardiolan ya yi, yana horas da 'yan wasan na Bayern Munich. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China