in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutumin da ya halaka sojin Birtaniya ya bayyana a kotu
2013-05-31 16:14:47 cri
A ranar 30 ga wata, Michael Adebowale da ake tuhumarsa da laifin kashe wani sojan Birtaniya a wata unguwar dake birnin Landan ya bayyana a gaban kotu, an kuma tuhume Mista Michael mai shekaru 22 da laifin kisan gilla da mallakar makamai ba bisa doka ba.

Bangaren 'yan sanda na London ya ce, an tuhume Michael Adebowale da kashe sojan Birtaniya mai suna Lee Rigby, haka kuma, da mallakar bindiga ta barauniyar hanya. A ranar 22 ga wata, yayin da aka cafke Adebowale, ya ji rauni, sannan an yi masa aikin jinya a asibitin, har zuwa ranar 28 ga wata, daga baya an kai shi wani ofishin 'yan sanda da ke kudancin birnin Landan. Hakazalika har yanzu wani mutum daban mai suna Michael Adebolajo kuma mai shekaru 28 da ake zargi yana asibiti.

Ya zuwa yanzu, ban da mutane 2 da ake tuhume su, 'yan sanda kuma sun cafke mutane 8 da ake zargi da hannu kan wannan batu, daga cikin su kuwa an yi belin mutane 6, yayin da aka saki sauran mutane 2.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China