Sanarwar ta ce, an tsare masu kiyaye zaman lafiya 21 a wurin dake kusa da kasar Sham a tudun Golan a safiyar wannan rana. Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da hakan inda kuma ya nemi a sake su nan da nan.
Ban da haka, Ban Ki-Moon ya yi gargadi ga bangarori daban-daban na kasar Sham cewa, aikin masu sa ido na MDD shi ne duba yadda kasar Sham da Isra'ila suke gudanar da yarjejeniyar hana shiga yankin da aka kebe karkashin jagorancin MDD domin samar da zaman lafiya, don haka ya kamata a tabbatar da zaman lafiya da 'yancin masu sa ido.
A wannan rana kuma, ministan harkokin waje na kasar Birtaniya William Hague ya ba da jawabi cewa, kasar za ta fara tallafawa kungiyar adawa da gwamnatin kasar Sham a fannin motocin yaki, tufafin kiyaye harsashi da dai sauran kayayyakin soja.
Wannan shi ne karo na farko da kasar Birtaniya ta bayyana matsayinta kan batun kasar Sham. William Hague ya yi bayani cewa, matakin da kasar ta dauka ya dace da halin da kasar Sham ke ciki na rashin samun jin kai.
A ganin kafofin yada labaru na kasar, matsayin da William Hague ya nuna na bayyana cewa manufar da kasar ta dauka kan batun kasar Sham ta canja. (Amina)