in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da yaki da 'yan fashin teku a yankin ruwan Afirka
2013-12-27 15:58:23 cri

Mataimakin kwamandan sojojin ruwan kasar Sin Ding Yiping ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tura jiragen ruwa da za su rika yiwa manyan jiragen dake bin tekun Aden da yankin ruwan Somaliya rakiya, ta yadda kasar za ta sauke nauyin da ke wuyanta a harkokin kasa da kasa.

Jami'in ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin bikin cika shekaru biyar da rukunin farko na Sin ya gudanar da aikin rakiyar. Ya ce, masu fashin tekun suna kara yin barna tare da yin amfani da makamai, wannan ya sa za a dauki lokaci mai tsawo, ana kara karfin dakarun.

Ding ya ce, a shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta tura jiragen ruwa har sau 16 da suka kunshi jiragen ruwan yaki 42 zuwa tekun Aden da yankin ruwan Somaliya, don yiwa jiragen dakon kaya 5,465 rakiya tare da kwato jiragen da 'yan fashi tekun suka kwace guda 42, Kuma kimanin jiragen ruwa 13,214 ne suka shiga cikin shirin yiwa jiragen rakiya.

Bayanai na nuna cewa, ayyukan 'yan fashin teku, sun ragu matuka, sakamakon, matakan da kasashe daban-daban suka dauka na yiwa jiragen rakiya, inda a wannan shekara, aka samu rahotannin ayyukan 'yan fashin teku 11 kawai, ko da yake babu wanda ya yi nasara.

Jami'in na Sin ya ce, sojojin ruwa za su fadada shirin, tare da karfafa yin hadin gwiwa da dakarun kasa da kasa don tabbatar da zaman lafiya a duniya da shiyya-shiyya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China