Babban magatakardar MDD Ban Ki- moon ya bayyana cewa, tekuna da manyan ruwaye dake fadin duniya na da rawar takawa, wajen cimma muradun karni dake kunshe cikin manufofin ci gaba bayan shekara ta 2015.
Cikin jawabin da ya gabatar gaban mahalarta taron MDD game da dokokin teku, Mr. Ban ya ce, al'ummun duniya na dogaro kan tekuna, wajen samun abinci da ayyukan yi, don haka a cewar sa, ya zama tilas, a mai da hankali wajen kiyaye manyan ruwaye ta hanyar amfani da dokokin da suka dace.
Kaza lika babban magatakardar MDDr ya ce, dole ne a dauki matakan dakile matsin lambar da manyan ruwaye ke fuskanta, da hana su fiye da kima, da dakatar da gurbata ruwa da sinadarai masu hadari, da kuma kandagarkin matsalar sauyin yanayi. Daga nan sai ya ja hankalin kasashe masu ruwa da tsaki game da dokar kariya ga manyan ruwaye ta UNCLOS, da su ba da cikakken hadin kai domin samun nasarar da ake fata.
An dai bude taron na yini biyar ne a ranar Litinin, gabanin bikin tunawa da fara aiwatar da dokar ba da kariya ga manyan ruwaye ta duniya karo na 20. (Saminu)