Ayyukan 'yan fashin teku a ruwan Somaliya sun ragu sosai sakamakon taimakon sojojin ruwan kasashen waje dake ba da kariya, kamar yadda wata cibiya mai lura da wannan sashi a duniya ya bayyana cikin rahoton da ya fitar.
A cikin rahoton hukumar kula da harkokin teku ta kasa da kasa IMB, an nuna cewa, an samu ayyukan 'yan fashin tekun guda 15 kawai a shekarar da ta gabata wato 2013, abin da ya yi kasa da kashi 75 a cikin 100 a shekarar ta 2012, sannan 237 a shekarar 2011, wannan adadin ya nuna raguwar fashin teku sosai a duniya baki daya.
Darektan hukumar Pottengal Mukundan ya ce, babban dalilin da ya sa aka samu raguwar wannan muguwar sana'a ita ce raguwarta a kan ruwan Somaliya dake gabar ruwan gabashin Afrika.
Raguwar wannan wani abin farin ciki ne ga kamfanonin manyan jiragen ruwan jigilar kaya wadanda suke bi ta tekun Indiya kuma suka zama wadanda suka fi samun harin wanda wani lokacin sai sun biya diyya mai yawa kafin a saki kayayyakinsu ko ma'aikatansu.
'Yan fashin teku a yammacin Afrika sun yi kashi 19 a cikin 100 a duk duniya baki daya a shekarar da ta gabata, 'yan fashin teku daga Nigeriya da 'yan fashi da makami sun karbi kashi 31 a cikin 100 a yankin baki daya da ya zama kashi 51 a cikin 100, sannan suka kama mutane 49, suka yi garkuwa da su tare da sace mutane 36, adadin da ya haura duk shekara tun daga shekarar 2008. (Fatimah)