A cikin wannan rahoto, MDD da AU sun tabbatar da cewa sauya yanayin harkar masana'antu a Afrika ya kasa a yawancin dalili, domin kasashen Afrika sun yi amfani da wasu hanyoyin a fuskar masana'antu da suka rataya kan rashin kwazo da rashin daidai harkoki a matsayin koli, da kuma rashin shawarwari masu alfanu tare da bangarorin da abin ya shafa.
Duk da rahoton ya tabbatar da cewa an samu muhimmin ci gaban tattalin arziki a Afrika a tsawon karnin baya bayan nan bisa karuwar kayayyakin bukatun farko, kyautatuwar tsarin mulki na gari da kuma karuwar bukatun cikin gida da fadada dangantakar kasuwanci da zuba jari tare da kasashen ke samun ci gaban tattalin arziki. (Maman Ada)