in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun Unicef ya yi Allah-wadai da hare-haren da aka kaiwa yara a Syria
2014-05-01 16:51:44 cri
Asusun tallafawa yara na MDD(Unicef) ya bayyana rashin jin dadinsa kan jerin hare-haren babu gaira babu dalili da suka yi sanadiyar mutuwa da jikkatar yara da dama a kasar Syria.

Kalaman asusun sun zo ne kwana guda bayan da wasu jerin hare-hare guda uku da aka kai a kasar da yakin da aka shafe shekaru 4 ana yi a kasar ya daidaita.

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu harin rokoki da aka kai a Al-Shaghour da ke wajen birnin Damascus ya kashe tare da jikkata daliban wata makarantar koyon sana'o'i,baya ga yara 14 da suka mutu da kuma wasu sama da 80 da suka jikkata sanadiyar harin.

Bugu da kari wani harin roka da aka kai a A'dra da ke karkarar Damascus shi ma ya kashe yara 3 da ke zaune a wani wurin da aka tsugunar da wadanda yakin ya wargaza.

Har ila a wannan rana,wani bam da ya tashi a cikin wata mota a wani wuri mai cunkoson jama'a a birnin Homs, ya haddasa mutuwar a kalla mutane 100, ciki har da mata da yara da dama,baya ga wasu sama da mutane 100 da suka ji rauni.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China