Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar a jiya Talata, biyowa bayan bayyana sakamakon zaben kasar ta Masar, Mr. Ban ya ce ya maida hankali kwarai ga wannan sakamako na zaben da ya gudana daga 26 zuwa 28 ga watan Mayun da ya shude. Ya kuma yi imani da cewa, sabon shugaban kasar ta Masar zai yi kokari wajen biyan bukatun jama'ar kasar, musamman ma a fannin wanzar da zaman lafiya da wadata, da bunkasa dimokuradiyya a kasar.
Haka zalika sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya jaddada aniyar MDD ta ci gaba da bada gudummawa da goyon baya ga kasar Masar kamar yadda ta saba. (Zainab)