Hukumar zaben shugaban kasar Masar ta sanar a ranar Talata cewa, tsohon shugaban rundunar sojojin Masar, Abdel Fattah al-Sissi ya zama sabon shugaban kasar wannan kasar Larabawa mafiya yawan jama'a, bayan ya lashe zabe da babban rinjaye gaban abokin takararsa na jam'iyyar adawa Hamdeen Sabahy a tsawon kwanaki uku na zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen watan Mayu.
Dan takarar shugaban kasa Abdel Fattah Said Hussein Khalil al-Sissi ya samu kuri'un 23 780 104, kimanin kashi 96,91 cikin 100 na zaben, in ji shugaban hukumar zaben kasar Anwar al-Assi a yayin wani taron manema labarai, a yayin da 'dan takarar jam'iyyar adawa mista Sabahy ya samu kuri'un 757 511, kimanin kashi 3,1 cikin 100.
Fiye da mutane miliyan 25 daga cikin mutane miliyan 53,9 na Masar suka yi zabe, wanda ya ba da adadin halartar wannan zabe da kashi 47,45 cikin 100, in ji mista Al-Assi. (Maman Ada)