Misirawa sama da miliyan 53 ne ake sa ran za su kada kuri'unsu, yayin babban zaben kasar da za a yi a ranekun Litinin da Talatar nan. Zaben da zai zamo na farko a kasar tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Morsi.
Ana dai hasashen jagoran juyin mulkin sojin da ya gabata a kasar Abdel-Fattah al-Sisi ne zai lashe zaben da gagarumin rinjaye, inda ake zaton zai samu kuri'u sama da na abokin takararsa Hamdeen Sabahy, wanda ya zo na uku a yayin zaben kasar da ya gudana a shekarar 2012.
Rahotanni sun bayyana cewa, an bude runfunan zabe kimanin 11,000 a lardunan kasar 27, tun daga karfe 9 na safiyar Litinin, yayin da kuma alkalan kasar kimanin 15,000 ke aikin sanya ido ga gudanar zaben. Haka kuma an tura jami'an tsaro sama da 432,000 sassan kasar daban daban domin tabbatar da nasarar zaben.
A hannu guda kuma akwai wakilai masu sa ido daga kungiyar tarayyar Turai, da na AU, da kuma na kungiyar tarayyar Larabawa ta LA.
Zaben dai na zuwa ne a daidai lokacin da magoya bayan tsahon shugaban kasar Morsi, ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar kin jinin zaben a lardunan Giza, da Beheira da kuma Sharqiya.
Ana sa ran bayyana sakamakon zaben a ranar 5 ga watan Yuni mai zuwa. (Saminu)