Hukumar zabe mai zaman kanta dake kula da zaben shugaban kasa a kasar Masar ta dauki niyyar a ranar Talata ta kara lokacin zaben shugaban kasa da kwana daya, domin tabbatar da cewa, an kwashe kwanaki uku ana gudanar zabe a cikin wannan kasa, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar MENA.
Makasudin wannan mataki shi ne na baiwa karin masu zabe da ma sauran jama'ar kasar zuwa yankunansu na asali domin gudanar da zabensu yadda ya kamata, in ji wani mamban hukumar zabe da kamfanin dillancin labarai na MENA ya rawaito.
Gwamnatin Masar ta bayyana cewa, kwana na biyu na zabe zai kasancewa ranar hutu domin kara adadin halartar masu zabe jefa kuri'unsu.
Tsohon shugaban rundunar sojojin kasar Masar, Abdel-Fattah al-Sissi wanda ya kifar da tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi, shi ne ake ganin zai lashe wannan zabe bisa babban rinjaye gaban 'dan takarar jam'iyyar adawa, Hamdeen Sabahi wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasar Masar na shekarar 2012. (Maman Ada)