A kasar Masar, 'dan takarar zaben shugaban kasa kuma shugaban jam'iyyar adawa, Hamdeen Sabbahi ya amince a ranar Alhamis da kayen da ya sha a zaben shugaban kasar da aka kammala ranar Laraba, gaban abokin takararsa, tsohon shugaban rundunar sojojin kasar Masar, Abdel Fattah al-Sissi.
Na amince da rashin samun nasara a wannan takarar shugaban kasa, in ji Sabbahi a yayin wani taron manema labarai. Ya kuma ci gaba da cewa, muna ba da misali mai kyau da girmama ra'ayin al'ummar kasa.
Sakamakon farko sun nuna babban rinyajen mista Sissi, wanda ya samu kuri'un zabe fiye da kashi 90 cikin 100.
Amma duk da haka, Sabbahi ya yi allawadai da kura-kuran da aka samu a yayin wannan zabe, duk da cewa, wadannan matsaloli da aka samu ba za su kawo illa ga sakamakon zaben karshe ba. (Maman Ada)