Wata kotun kasar Masar ta yankewa magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi su 163 hukuncin dauri, bisa samun su da ta yi da laifin tada hargitsi a shekarar da ta gabata.
Kotun dai ta yankewa wadanda ake zargin hukuncin dauri daga shekaru 10 zuwa 15. Hakan kuma na zuwa ne kwanaki kalilan gabanin babban zaben kasar da aka tsara gudanarwa a ranekun 26 da 27 ga watan Mayu.
Kaza lika wata kotun kasar ta yankewa wasu 'yan kungiyar su 126 hukuncin daurin shekaru goma-goma a kurkuku, bisa samun su da laifin kaiwa wasu caji-ofis din 'yan sanda hari, da kuma tada hargitsi, biyowa bayan tumbuke shugaba Mohammed Morsi daga mukamin sa da sojoji suka yi a watan Yulin bara.
Wannan dai hukunci kari ne kan wasu mutane 37, da wata kotun dake zamanta a birnin Alkahira ta yankewa hukuncin daurin shekaru sha biyar, bisa samun su da laifin kaiwa tashar jirgin kasa dake lardin Giza hari, a watan Disambar shekarar da ta gabata.
A baya ma dai wata kotun kasar ta yankewa wasu magoya bayan tsohuwar gwamnatin ta Morsi su 700 hukuncin kisa, ko da yake dai wannan mataki ya sha suka daga sassan kasashen duniya.
Kafin hakan kuma mahukuntan kasar sun ayyana kungiyar ta 'yan uwa musulmi a matsayin haramtacciyar kungiya ta 'yan ta'adda. (Saminu)