A ganin bangarorin da suka halarci taron, dole nea kasar Iran ta gabatar da shirinta na nukiliya gaba daya a fili. Kuma bangarorin za su ci gaba da yin hadin gwiwa don sa kaimi ga Iran da ta koma teburin yin shawarwari. Bisa labarin da aka bayar, an ce, a gun taron da aka shirya a wannan rana, ayyukan hana kasar Iran fitar da man fetur zuwa kasashen waje da farashin makamashi na duniya sun zama manyan abubuwa da aka tattauna.
Kasar Iran ita ce kasa ta uku da ke fitar da man fetur zuwa kasashen waje. Idan ake hana kasar fitar da man fetur zuwa kasashen waje, ta farashin man fetur zai iya canjawa.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, kasar Iran ta gayyaci tawagar masanan hukumar IAEA da su kai ziyara a kasar, kuma tana son sake yin shawarwari kan batun nukiliya na kasar.