An yi asarar rayuka ta hanyar tashin hankali kisa kuma iyalai da dama da ma al'ummomin aka sanya cikin kuncin zaman rayuwa. Lokaci ya yi a fahimci yadda munanan laifuffuka suke lalata kasashen duniya, ta yaya ne suke shafar musamman ma matasa maza da mata, in ji darektan kula da harkokin jama'a na ONUDC, mista Jean Luc Lemahieu a yayin bikin gabatar da wannan bincike a birnin London. (Maman Ada)