Wannan harka ce ta dangantaka tsakanin kasashen biyu kuma MDD tana fatan ganin an warware matsalar ta hanyar dangantaka, in ji mista Stephane Dujarric, kakakin MDD a yayin wani taron manema labarai a lokacin da aka aza masa tambaya kan matakin MDD game da kiyawar Amurka ga ba da sabon visa ga sabon wakilin kasar Iran a MDD.
MDD ba ta fito karara ta nuna damuwarta ba kan wannan matsala, in ji mista Dujarric, inda kuma ya kara da cewa yarjejeniya tare kasar dake karbar bakunci kundi ne na jama'a dake bayyana karara nauyin da ya rataya.
Bisa wannan yarjejeniya, a matsayin kasa mai karbar bakuncin MDD, ya dace Amurka ta tabbatar da 'yancin mutanen da aka gayyato cibiyar MDD dake birnin New York. (Maman Ada)