Geng ya sanar da hakan ne a taron manema labaru na ma'aikatar tsaron kasar da aka yi a yau, inda ya bayyana cewa, a yayin wannan taro, Wang zai yi jawabi, domin bayyana ra'ayin tsaron Asiya da shugaba Xi na kasar Sin ya gabatar a taron koli na inganta cudanya da karfafa hadin gwiwa ta nahiyar Asiya, da gabatar da ayyukan da rundunonin sojan Sin suka yi domin tabbatar da wannan ra'ayi na tsaron Asiya da yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya a fannin tsaro, kuma Wang ya zai yi kira dagabatar da kirayinsa na a karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro tsakanin shiyya-shiyya.
Ban da haka, an labarta cewa, a yayin taron, Wang zai gana da shugabannin hukumomin tsaron kasa da Janar din rundunonin soja na wasu sauran kasashen duniya da abin ya shafa, domin yin musayar ra'ayi kan yanayin tsaro na shiyya-shiyya da dangantakar a tsakanin rundunonin sojansu.(Fatima)