Bisa labarin da aka bayar, an ce, yanzu gwamnatin Sin tana yin nazari kan tsaron na'urar IBM da ake amfani da ita.
Game da wannan batu, a gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Qin Gang ya furta cewa, a zamanin yau, tsaron yanar gizo ta intanet da tsaron sakwanni na da muhimmanci kwarai da gaske ga tsaron kasa. Shi ya sa gwamnatin Sin za ta gabatar da ka'idojin da abin ya shafa nan ba da dadewa ba, a kokarin kara tabbatar da tsaro a wadannan fannoni. (Fatima)