Hakan dai ya biyo bayan wani taro da aka gudanar a kasar Faransa kan tsaron tarayyar Najeriya a jiya Asabar. Taron da ya samu halartar shugabannin kasashen Najeriya, da Chad, da Kamaru, da Nijar, da Benin, da Faransa, baya ga wasu manyan kusoshin kasashen Turai da Amurka wadanda suka albarkanci taron.
Cikin jawabinsa yayin taron, shugaban Goodluck Jonathan na Najeriya ya ce, a yanzu haka kungiyar Boko Haram ta wuce matsayin kungiyar 'yan ta'adda, a cewarsa kungiyar ta zamo tamkar Alqa'ida a yammacin Afirka. Shugaba Jonathan ya kara da cewa shugabannin yammacin Afirka sun yi alkawarin hada kai da juna, ganin wajibcin hakan wajen dakile ayyukan wannan kungiya.(Bello Wang)