in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron manyan jami'an kungiyar 'yan ba ruwanmu karo na 16
2012-08-28 11:15:06 cri

Jiya ranar 27 ga wannan wata da dare, aka rufe taron manyan jami'an kungiyar 'yan ba ruwanmu karo na 16 a Tehran, babban birnin kasar Iran. A yayin taron, an zartas da daftarin da za a gabatar wa taron ministocin harkokin waje na taron kolin kungiyar 'yan ba ruwanmu domin tattaunawa.

A yayin taron manema labarai da aka shirya bayan rufe taron, babban sakataren wannan taron manyan jami'ai kuma mataimakin ministan harkokin waje na kasar Iran Medhi Akhundzadeh ya yi bayani kan wasu abubuwan da suka shafi wannan daftarin.

Daftarin da aka cimma ya yi kira ga kasa da kasa da su rage yawan makaman kare dangi, ingiza gudanarwar kwance damarar makaman nukiliya tare kuma da cimma burin hana kera makaman nukiliya a yankin gabas ta tsakiya.

Daftarin ya bayyaya cewa, ya kamata kasashen duniya daban daban su shiga aikin tafiyar da tsarin kasa da kasa tare, kana su nuna kiyayya kan ra'ayin nuna karfin tuwo na wata babbar kasa a duniya da wasu kasashen yamma, musamman ma kasar Amurka suka dauka. Haka kuma Daftarin ya nuna adawa da wasu kasashe su yi amfani da ma'auni iri biyu yayin da suke gudanar da harkokin kasa da kasa bisa zargin yaki da ayyukan ta'adanci, lamarin dake kawo barazana ga zaman lafiya a duk fadin kasa da kasa.

Ban da wannan kuma daftarin ya nuna kiyayya ga takunkumin da aka sanya kan wata kasa a gefe daya da rashin yarda ga wasu matakan da Isra'ila ta dauka kan batun Palestinu, kuma ya jaddada cewa, kamata ya yi a nuna kwazo da himma kan aikin yaki da ta'addanci.

Za a kira taron ministocin harkokin waje na taron kolin kungiyar 'yan ba ruwanmu daga ranar 28 zuwa ta 29 ga wannan wata, daga baya, za a shirya taron shugabannin kungiyar daga ranar 30 zuwa ta 31.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China