A bikin bude taron, shugaba Mohamed Morsi na kasar Masar ya mika ikon shugabancin kungiyar a hannun Iran. Ya bayyana fatansa cewa, Iran za ta shugabanci kungiyar yadda ya kamata, tare da inganta rawar da kungiyar ke takawa a duk duniya. Ya kara da cewa, tun can da kuma zuwa yanzu kungiyar na taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da adalci a duniya da goyon bayan kasashe masu tasowa. Mohamed Morsi ya yi kira ga kungiyar da ta kyautata kanta, ci gaba da mara wa kasashe masu tasowa baya, kara azama kan wanzar da adalci da zaman lafiya a duniya, a kokarin taka rawa mai kyau a tsarin kasa da kasa.
A jawabinsa a bikin, Ali Khamenei, shugaban addini na Iran ya ce, kasarsa ba za ta yi watsi da ikon yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana ba. Sa'an nan kuma Ban Ki-moon, babban magatakardan MDD ya kalubalanci Iran da ta dauki matakai domin kau da damuwar kasashen duniya kan shirinta na nukiliya.(Tasallah)