Mista Ma ya kara da cewa, kungyiar NAM, wata alama ce ta hada kan kasashe masu tasowa domin kyautata karfinsu, haka kuma tana da muhimmanci sosai wajen kiyaye zaman lafiya da kara kuzari kan samun ci gaba a duniya. Kasar Sin na sa ido kan kungiyar NAM, tare da nuna goyon baya kan manufarta da ka'idojinta har kullum, tana kuma dora muhimmanci kan ganin kungiyar NAM ta taka rawa mai yakini a cikin al'amuran kasa da kasa. A sa'i daya kuma, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan inganta rawar da MDD take takawa, tare da nacewa ga tanade-tanaden da ke cikin kundin tsarin MDD, a kokarin kara azama kan sanya dimokuradiyya cikin dangantaka a tsakanin kasa da kasa da daidaita al'amura cikin hadin gwiwar kasa da kasa.
Har wa yau kuma, mista Ma ya nuna cewa, yanzu ana gazawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata, kana ana fama da matsaloli wajen samun bunkasuwa. Kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kara yin gyare-gyare kan tsarin da ake bi wajen tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya, kara ba wa kasashe masu tasowa da masu matsayin sabbin kasuwanni wakilci da ikon bayyana ra'ayoyinsu, yin gyare-gyare kan tsarin kudi na duniya tare da sa kaimi kan hada kan kasa da kasa wajen samun ci gaba, a kokarin kawar da rashin daidaito a tsakanin kasashe masu sukuni da masu tasowa ta fuskar samun bunkasuwa. Dadin dadawa kuma, kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya, musamman ma kasashe masu sukuni da su cika alkawari na kara baiwa kasashe mafi fama da rashin ci gaba taimako da rage basusukan da ke binsu, a kokarin ba da gudummowa wajen ganin kasashe masu tasowa sun tabbatar da manufar MDGs, wadda MDD ta tsara kan batun ci gaba a shekarar 2000. (Tasallah)