A gun bikin bude wannan haduwa, ministan harkokin waje na kasar Iran Ali Akabar Salehi ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashe membobin kungiyar 'yan ba-ruwanmu su ci gaba da aiwatar da ayyukan da kasashe farko wadannan da suka kirkiro kungiyar suka yi, da sa kaimi ga samun zaman lafiya da na karko a dukkan duniya. Salehi ya gabatar da shawarwari 8, wato kawar da wariya da aka nunawa al'adun kasa da kasa, yaki da ta'addanci, rage makaman nukiliya, kiyaye hakkin dan Adam da dai sauransu. Game da batun Palesdinu, Salehi ya ce, idan kasar Isra'ila ta ci gaba da samun goyon baya daga kasashen yammacin duniya to har abada ba za a samu zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ba. (Zainab)