Shugaban taron wannan karo, kuma shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad, ya ce takardun da aka zartas sun hada da 'sanarwar Tehran', dake kunshe da batun cigaba da nuna goyon baya ga Palesdinu, da dai makamantansu. Ban da haka, an tsai da kudurin kira taron shugabannin kungiyar karon 17 a kasar Venezuela a shekarar 2015.
A cewar shugaba Ahmadinejad, mahalarta taron sun yarda da dukufa kan kokarin cimma burin kungiyar 'yan ba ruwanmu, kana sun yi kira da a yi kwaskwarima kan tsarin da ake bi wajen kula da harkokin duniya, ta yadda za a sanya dukkan kasashen duniya su shiga wannan aiki, don tabbatar da zaman lafiya a duniya. Har ila yau, mahalarta taron sun amince da kare hakkin bil Adama, da tabbatar da mutuncin mutum, gami da kokarin magance tashin hankali. (Bello Wang)