Kafofin watsa labaran na gwamnati sun ruwaito wani jami'in soji, wanda ba'a tantance ba na cewar "bayan gudanar da hare-hare dabam dabam, sojojin Syria da kuma rundunar dakarun kariya na kasa sun kara wanzar da tsaro da zaman lafiya a birnin Yabroud da kuma arewacin wajen garin Damascus, bayan da aka kashe 'yan ta'adda da yawa wadanda ke birnin, kuma suna amfani da birnin wajen wucewa da makamai da kuma 'yan ta'adda ya zuwa Syria.
Kame garin Yabroud wanda shi ne babban cibiyar 'yan tawaye kusa da kan iyaka na Lebanon, yana iya sanadiyyar cushe kafofin samar da kayayyaki na 'yan tawaye.
Wannan kuma na nufin gwamnatin kasar ta wanzar da ikon wani babbban yanki tun daga Damascus ya zuwa tsakkiyyar birnin Homs. (Suwaiba)