in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da Ban Ki-Moon
2014-05-19 15:52:27 cri

Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya gana da babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a Litinin din nan 19 ga watan Mayu a birnin Shanghai. Gabanin gudanar babban taron tattaunawa kan inganta cudanya da karfafa hadin gwiwa a nahiyar Asiya na CICA.

Yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya ce, shekara mai zuwa shekara ce ta cikon shekaru 70, da samun nasarar yaki da nuna kyamar wani bangare na al'ummar duniya, da kuma yakin kin jinin harin Japanawa na jama'ar kasar Sin, haka kuma shekaru ta 70 da kafuwar MDD.

Don haka ya ce kamata ya yi kasashen duniya, su yi kokari tare don sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a dukkanin sassan duniya. Shugaba Xi ya ce, da farko ya kamata a tsaya tsayin daka wajen daidaita rikice-rikice a siyasance, na biyu, a sa himma wajen samun bunkasuwa tare, na uku, a kara kaimi a fannin bada jagorancin MDD bisa harkokin duniya.

Shi kuwa a nasa bangare Mr. Ban Ki-Moon cewa ya yi, MDD na godiya ga kasar Sin, game da gudummawar da ta bayar kan batutuwa da dama, da shigar ta harkokin MDD cikin yakini. Ya ce hakikanin abubuwan dake faruwa sun shaida cewa, kasar Sin ta zama wata ingantacciyar abokiyar hadin kan MDD.

Taron koli game da tattaunawa kan inganta cudanya, da karfafa hadin gwiwa a nahiyar Asiya na CICA na bana, wanda kasar Sin ta karbi bakoncin sa, zai sa kaimi ga kasashen Asiya, wajen ba su damar kara amincewa da juna, da bunkasa hadin kansu, tare da tinkarar kalubale a fannin tsaro. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China