in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barcelona ta sanar da sabunta yarjejeniyarta da Messi
2014-05-20 14:58:27 cri
A ranar Jumma'a 16 ga watan nan na Mayu ne mahukuntan kulaf din Barcelona na Sifaniya, suka sanar da cimma yarjejeniyar sabunta kwantiragin dan wasan gaban kungiyar Lionel Messi.

Kungiyar Barcelona wadda ta sanar da labarin a shafin ta na yanar gizonta, ta kuma ce nan da 'yan kwanaki Messi tare da mahukuntan kulaf din za su sanya hannu kan sabuwar kwangilar da aka cimma.

Ko da yake kulob din bai fayyace bayani kan wannan batu ba tukuna, amma ana sa ran sabuwar kwangilar za ta baiwa Messi damar zama dan wasan kwallon kafa mafi samun albashi a duniya, inda yawan kudin da zai samu a ko wace shekara zai kai kimanin dalar Amurka miliyan 27.4, adadin da zai haura albashin Cristiano Ronaldo bisa sabuwar kwangilar da ya kulla da Real Madrid.

Lionel Messi wanda shekarunsa za su kai 27 a duniya a watan Yuni mai zuwa, ya riga ya buga wasanni 424 a matsayin daya daga cikin 'yan wasan Barcelona, inda ya ci wa kulaf din kwallaye 354. Matakin da ya sanya shi dara duk wani dan wasan kulaf, a yawan kwallayen da ya ciwa Barcelona. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China