Wasan da kungiyoyin 2 suka buga a filin wasan Camp Nou dake birnin Barcelona ya yi zafi kwarai da gaske, ganin yadda 'yan wasa daga bangarorin 2 suka yi ta dauki-ba-dadi kafin kaiwa ga karshen wasan. Musamman ma bangaren Atletico, ganin yadda 'yan wasanta 2 kwararru Diego Costa da Turan suka samu raunuka cikin mituna 20 da take wasa.
Dan wasan Barcelona Alexis ne dai ya ci wa kungiyar sa kwallo tun kafin tafiya hutun rabin lokaci, kwallon da ta kusa kaiwa ga baiwa Barcelona damar lashe wannan wasa, duba da cewa a wasan zagayen farko ma kungiyoyin biyu sun tashi kunnen doki a gidan Atlantico Madrid.
Sai dai bayan hutun rabin lokaci labara ya sha ban ban, yayain da dan wasan Atletico Godin ya samu nasarar farke kwallon da aka jefawa kungiyar ta su, aka kuma tashi haka, lamarin da ya baiwa Atletico damar da take nema ta zama zakara a gasar ta La Liga.
Idan aka koma ga tarihi, za a ga cewa Barcelona ta taba lashe wannan kofi na La Liga ne har sau 22, yayin da a nata bangare Atletico ta zama zakaran gasar karo 9.(Bello Wang)