140522-kungiyar-kwallon-kafar-mata-ta-kasar-sin-ta-samu-tikitin-halartar-gasar-cin-kofin-duniya-bello
|
Kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Sin ta zama kungiya ta farko, da ta samu tikitin halartar gasar cin kofin duniya ta mata da za ta gudana a kasar Canada a shekara mai zuwa.
Kungiyar Sin ta samu wannan dama ne biyan ta lashe takwararta ta kasar Myanmar da ci 3 da nema, a wasan zagaye na 2 na gasar cin kofin nahiyar Asiya ta mata a ranar Asabar 17 ga wata.
An yi wasan ne a filin wasan Thong Nhat dake birnin Ho Chi Ming na kasar Vietnam, inda 'yan wasan kasar Sin Ren Guixin, Ma Xiaoxu da Yang Li ko waccensu ta samu jefa kwallo guda a raga, yayin da 'yan wasan Myanmar a nasu bangaren suka yi iyakacin kokari, wajen kare gidansu ba tare da cimma nasarar jefa kwallo ko guda a raga ba.
Wannan nasara dai kari ce bisa yadda Sin ta lashe Thailand da ci 7 da nema, a wasanta na farko, nasarar da kuma ta sanya kungiyar kasar Sin, wadda ta taba zama zakaran nahiyar Asiya karo 8, samun damar halartar wasan kungiyoyi 4 na gasar cin kofin Asiya a wannan karo.
Bayan da aka tashi wasan, Chetan Kulkarni, kakakin hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Asiya, ya taya kungiyar kasar ta Sin murnar samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta shekara mai zuwa, ya na mai cewa kungiyar ce ta farko tsakanin kungiyoyin kasashe daban daban, da ta samu wannan dama ta halartar gasar cin kofin na duniya.
Bisa tsarin gasar cin kofin duniya ta mata dai, kungiyoyi 4 da ke kan gaba a gasar cin kofin nahiya Asiya a bana, za su samu damar shiga gasar ta shekara mai zuwa kai tsaye.
Baya ga kasar Sin wadda ta lashe Myanmar, itama Koriya ta Kudu a nata bangare ta lashe Thailand da ci 4 da nema, inda ta samu damar halartar gasar cin kofin duniya ta mata dake tafe. (Bello Wang)