140515-forbes-ta-gabatar-da-jerin-sunayen-yan-wasan-kwallon-kafa-da-suka-fi-samun-kudin-shiga-bello
|
A 'yan kwanakin baya Mujallar Forbes ta gabatar da jerin sunayen 'yan wasan kwallon kafa da suka fi samun kudin shiga a shekarar 2013, inda ta bayyana dan wasan kwallon kafan Real Madrid Cristiano Ronaldo, a matsayin lamba daya a wannan fanni, yayin da Lionel Andrés Messi ke biye masa a matsayi na biyu, sai kuma Zlatan Ibrahimovic dake a matsayi na uku.
Wannan bayani dai da mujallar ta Forbes ta fitar ya kunshi kudin shiga, da kudin lambar yabo, da kudin da 'yan wasan suka samu yayin tallace-tallace, amma ba a sanya kudin sauyin kungiyoyi ba a ciki. An ce wadannan 'yan wasa su kai ga matsayin da David Beckham ya taba hawa a baya na kasancewa a matsayin farko cikin dogon lokaci kafin ya yi ritaya.
Cristiano Ronaldo ya zama dan wasan kwallon kafa da ya fi samun kudi shiga a shekarar 2013, saboda kwarewarsa yawan kudin shigarsa a shekarar bara ya kai dala miliyan 73.
A wata takardar jerin sunaye ta daban da Forbes din ta gabatar a fagen wasan Golf kuwa, Eldrick "Tiger" Woods ya sami kudin shiga dala miliyan 78.1, wanda kuma ya kasance a matsayin farko a wannan matsayi. (Amina)